Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Kwaikwayi Rasha Wajen Yi Wa Amurka Kutse Ta Yanar Gizo


Kasar China na yin amfani da wasu dabaru wajen kai wa Amurka hare-hare ta yanar gizo, da nufin tattaro bayanan wasu kwamitocin gudanarwa na jam'iyyun siyasa.

Mai yiwuwa kasar China ta kwaikwayi yadda Rasha ta yi katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016, wadda ke kai wasu hare-hare kan kwamitocin gudanarwa na jam’iyyun siyasa da wasu kwararru daban-daban ta hanyar aika musu da sakonnin email irin na kutse.

Wani kamfanin tsaron yanar gizo mai zaman kansa FireEye, shine ya gano hakan, sai dai har yanzu akwai wasu batutuwan da ba a tantance ba - - kamar irin bayanan da China ta samo a dalilin kutsen da ta yi, da kuma yadda za ta yi amfani da bayanan, har yanzu dai babu masaniya.

Kamfanin FireEye ya fadawa Muryar Amurka ta sakon email cewa, “Har yanzu dai cikin hare-haren da ake kaiwa bamu gano abin da ake son cimmawa ba.”

Ya zuwa yanzu dai jami’an gwamnatin Trump sunyi shiru kan wannan batu, suna masu alkawarin bayyyana bayanai cikin mako mai zuwa a jawabin da mataimakin shugaban kasa Mike Pence zai yi a nan birnin Washington.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG