Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Kwamitin Shari'a Zasu yanke Hukunci akan Kavanaugh


The Senate Judiciary Committee conducts business on the nomination of Supreme Court nominee Judge Brett Kavanaugh, Sept. 28, 2018, on Capitol Hill in Washington.
The Senate Judiciary Committee conducts business on the nomination of Supreme Court nominee Judge Brett Kavanaugh, Sept. 28, 2018, on Capitol Hill in Washington.

Wakilan jam’iayar republican su goma 11 da yan democrats su 10, ne zasu yanke hukunci akan tabbatar da nadin Kavanaugh a matsayin alkalin kotun koli

Kwamitin shari’ar majalissar dattawa Amurka sun shirya jefa kuri’a akan wanda zai cike gurbin alkalen kotin kolin Amurka Brett Kavanough a yau juma’a, bayan jiya Alhamis an yini ana sauraran laifin da ake zargin shi, da Christine Blasey Ford ta gabatar akan laifin keta haddin ta.

Yan jam’iayar republican su goma 11 da yan democrats su 10, sune zasu yanke hukuncin ko su bada shawarar dukkan wakilan Majalisar su amince ko kuma a’a, inda ake sa ran fara shirin jefa kuri;ar a ranar asabar.

Amma Kungiyar lauyoyin Amurka jiya Alhamis da yamma ta bukaci yan majalissun su jinkirta zaben har sai hukumar bincike manyan laifu ta Amurka wato FBI, ta kara wani sabon bincike akan zargin da Ford da sauran matan sukai mashi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG