Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cece-ku-ce Tsakanin Amurka Da China Game da Cinikayya Na Kara Zafi


Shugaba Trump na Amurka da Shugaba Xi (Shi) na kasar China
Shugaba Trump na Amurka da Shugaba Xi (Shi) na kasar China

Duk da cewa bangarorin biyu sun jaddada cewa ana cigaba da yin shawarwari, babu wani abu a zahiri da ke nuna su na kokarin neman mafita daga cece-kucen nasu.

A yayin da rikicin cinikayya tsakanin Amurka da China ke kara zafi, kasashen biyu na maganganu masu zafi amma kuma, a lokaci guda suna ba da tabbacin cewa komai zai daidaita.

Duk da tabbacin da ake samu daga kasashen biyu, masu fashin baki a China da Amurka sun rarrabu akan munin yanayin.

“A yanzu, kasuwanni na maida murtani, manoma na maida murtani, kungiyoyin cinikayya na maida murtani, kuma yawancin mu na ganin cewa karshenta, da kyar wannan takaddamar ta haifar da Da-mai-ido,” a cewar Dave Swenson wani masanin harkokin tattalin arziki a jami’ar Iowa dake Amurka. Ya cigaba da cewa, “abinda muke gani yanzu tabbas rikici ne, an ja daga, abinda ba mu sani ba, shine har zuwa wane mataki bangarorin biyu zasu kai.”

Ana sa ran shugaba Trump zai sanar da sabon tsarinsa na haraji da zummar horad da China a kan irin manufofinta na musaya da kuma satar fasahun Amurka da take yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG