Za'a haska fitila kan dangantakar Amurka da kawayenta a kungiyar tsaro ta NATO a wannan makon, lokacinda shugaban Amurka Donald Trump zai jagoranci taron koli da kasashen da suke yankin Baltic a fadar White House yau Talata.
Kamar yadda bayanai daga fadar white suke nunawa, shugaba Trump tareda shugaba Kersti Kaljulaid na Estonia, da shugaba Raimonds Vejonis,na Lativa, da shugaba Dalia Grybauskaita ta Lithuania sun kimtsa su gudanar da shawarwari don karfafa tsaro, cinikayya, da makamashi, da al'adu tsakanin Amurka da wadannan kasashe kawayenta a kungiyar tsaro ta NATO.
Haka nan fadar ta shugaban Amurka tace taron shugabannin zai nuna irin nasarori da kasashen suka samu wajen cika alkawarin bunkasa kudade da suke ware wa domin tsaro kamar yarjejeniyar da suka kulla a karkashin kungiyar ta NATO.
A farkon kama aikinsa, shugaba Trump, ya sha sukar kasashen dake cikin kungiyar tsaron ta NATO domin sun kasa ware kashi biyu cikin dari domin harkokin tsaro.
Facebook Forum