Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Laftanar-Janar Yusuf Buratai mai ritaya, a matsayin jakadan kasar a Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriyar.
Buratai shi ne tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya wadanda aka sauke su a watan Janairun bana.
Kazalika, an nada Janar Abayomi Gabriel Olonisakin mai ritaya wanda shi ne tsohon hafsan hafsoshin Najeriya a matsayin jakadan kasar a Kamaru wacce ita ma makwabciya ce ga Najeriyar.
A wani dan kwaryakwaryan biki da aka yi a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya a Abuja, Minista Geoffery Enyeama ya mikawa Buratai da Olonisakin wasikun tabbatar masu da mukamansu.
Tun dai a watan Fabrairun da ya gabata, Shugaba Buhari, ya mika sunayen tsoffin manyan hafsoshin sojin kasar hudu ga majalisar dokoki don a tantance su a matsayin jakadu.
Sauran biyun sun hada da Vice Adminiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya da Air Marshal Sadique Abubakar mai ritaya
Amma ya zuwa yanzu Buratai da Olonisakin kawai aka nada.