‘Yan Najeriya sun shiga bayyana ra’ayoyinsu nan da nan bayan sauke manyan hafsoshin sojin Najeriya tare da yin masu ritaya da kuma maye gurbinsu da sabbi. Ra’ayoyin sun kama daga masu nuna cancantar hakan zuwa masu ganin an yi ba a yi ba, ganin cewa an maye gurbin na da ne da wadanda su ma su ka kasa.
Masu takaicin irin hafsoshin da aka nada din, sun yi nuni da yadda su ka kwashe shekaru 11 ba tare da kawo karshen kungiyar Boko Haram ba da kuma sauran matsalolin da aka fuskanta na tsaro, ciki har da na garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ce ta fi fama da irin wadannan matsalolin.
Kanar Hussaini Manguno (ritaya), mai sharhi kan al’amuran tsaro, ya ce wannan canjin ya dace; ya kara da cewa dama tsoffin sojojin sun tare wuri ma jami’an sojin da ke biye da su. Ya ce an dan yi nasara, duk dayake babu yawa – saboda kimanin kashi 20% na nasara ne kawai aka yi.
Wani dan jahar Borno mai suna Abdullahi Alhassan, ya ce ganin harkar tsaro mashahuriya ce, idan aka lura da yadda ake ta samun matsalar rashin tsaro ciki har da hare haren ‘yan Boko Haram, kamar sam babu ma shugabancin a bangaren tsaro. Ya ce shi kansa Janar Buratai akwai wasu hanyoyin garinsu da bai iya bi.
Shi ma wani mai suna Abubakar Ladan, ya ce lallai Shugaba Buhari ya cancanci yabo, ganin cewa bayan da aka yi ta kururuwan a sauke manyan hafsoshin ya saurari jama’a amma bai gaggauta sauke su ba, sai bayan da ma aka manta. Ya ce ga dukkan alamu wannan canjin zai amfani jama’a.
Ga dai Haruna Dauda da rahotonsa ta sauti: