Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Tabbatar Da Tsofaffin Hafsoshin Soji A Matsayin Jakadu


Zaman Majalisar dattijai na tantance hafsoshin sojin Najeriya
Zaman Majalisar dattijai na tantance hafsoshin sojin Najeriya

Majalisar Dattijai ta tabbatar da tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya sauke a matsayin jakadu.

Wadanda aka tabbatar su ne tsohon babban hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai; Babban Hafsan tsaro Janar General Abayomi Olonisakin; Babban hafsan mayakan ruwa, Vice Admiral Ibok Ete Ibas; Babban hafsan mayakan sama, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma tsohon babban jami’in tsaro mai kula da harkokin liken asiri, Air Vice Marshall Muhammad Usman.

Zaman Majalisar dattijai na tantance hafsoshin sojin Najeriya
Zaman Majalisar dattijai na tantance hafsoshin sojin Najeriya

Majalisar ta tabbatar da basu mukaman ne bayan zaman kwamitin harkokin kasashen ketare da dan majalisar dattijai Adamu Mohammad Bulkachuwa ya jagoranta.

Yanzu haka majalisar dattijan tana zaman tantance jami’an sojin da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba da za su maye gurbinsu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG