Kungiyar Lafiya ta duniya tace, mutane da dama sun mutu a sakamakon bular anobar Ebola data boye a wata gunduma dake gabashin kasar Saliyo.
Kungiyar tace masu bincike da aka tura gundumar Kono dake cikin lungu a makon jiya, sun gano yadda wadanda suka kamu da Ebola suke mutuwa a Asibitin da bashi da kayayyakin aikin tinkarar kwayar cutar. Masu binciken sunce cikin kwanaki goma sha daya sun bizne gawarwarkin mutane tamanin da bakwai wadanda cutar ta kashe, ciki harda wata nas da wani direban motar daukan mara lafiya da kuma wani wanda shine yake fitar da gawarwarki daga asibitin.
Kafin kungiyar Lafiya ta Duniya ta gabatar da wannan sanarwa a jiya Laraba da dare, sai data fara baiyana cewa yanzu kasar Saliyo, ta zarce sauran kasashe da yawan wadanda suke kamuwa da cutar da kuma wadanda cutar ke kashewa a Afrika ta yamma.
A wani labarin kuma, Mujjalar Time ta baiyana dukkan wadanda suke yaki da Ebola a zaman fitattun mutanen wannan shekara.
Jiya Laraba editar Mujallar Nancy Gibbs tayi bayanin cewa nas nasa da likitoci, wadanda a shirye suke su fito suyi yaki da wannan cuta, sun cancanci wannan karamci.
Tace, mutane ne dake bugun kirji suna sadaukar da rayukansu a yayinda suke ceton wadansu, wadanda a wasu lokutan ma su kan harbu da kwayar cutar harma ta kashe su.
Mai magana da yawun fadar shugaban Amirka ta White House, John Earnest yace shugaba Barack Obama yana alfahari da mutane da suke sadaukar da rayukansu domin ceton wasu wajen yaki da cutar Ebola. Kuma yayi farin cikin ganin cewa sun samu wannan yabo da suka cancanci samu daga Mujallar Time.