Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liberiya Zata Tabbatar Bata Sake Samun Sabbin Kamuwa da Cutar Ebola Ba


Mai jinyar masu cutar ebola a Liberiya
Mai jinyar masu cutar ebola a Liberiya

Shugabar kasar Liberiya na fatan kasar ba zata sake samun sabbin kamuwa da cutar ebola ba nan da zuwa ranar kirsimeti

Liberiya Kasar Yammacin Afirka da cutar Ebola ta fi addaba ta sha alwashin ganin ba’a sake samun sabon kamuwa da cutar ba nan da zuwa ga 25 ga watan Disamba.

Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ta fada a wani jawabin da aka yada a fadin kasar a jiya Lahadi cewa kokarin kasar na murmurewa zai kasance da wahala. Ta ce dole ne bangaren lafiya na kasar ya dau karin matakan tinkarar bullar annobar cuta sannan ana kuma bukatar karin cigaba sosai a bangarorin gwamnati da kuma tattalin arzikin kasar.

Daga cikin adadin macemace 5,165 da su ka auku a Yammacin Afrika sanadiyyar Ebola, guda 2,800 daga Liberia ne.

Haka zalika a jiya Lahadi, jami'an kiwon lafiyar Amurka, sun ce matafiya daga Mali za su fuskanci irin tantancewa da kuma sa-idon da ake ma masu isowa daga Liberia da Saliyo da Guinea. Wannan kuwa ya hada da auna zafin jikin masu shigowa da kuma yi masu tambayoyi game da lafiyarsu da kuma yiwuwar kasancewa kusa da mai cutar Ebola.

Kodayake Mali bata fada cikin annobar ebola ba amma ana samun masu kamuwa jefi jefi.

XS
SM
MD
LG