Bayan aikin hajjin, hukumar dake kula da alhazan da suka fito daga kasashen Afirka, ta shiryawa alhazan liyafa inda alhazan Sokoto da Kano suka samu lambar yabon alhazai mafi natsuwa.
Bana alhazai dubu 166 suka fito daga nahiyar Afirka da ba larabawa ba. Najeriya ke da nafi yawan alhazai su dubu 76.Amma cutar ebola ta rage mutanen da suka so zuwa hajjin bana domin an dakatar da mutane daga kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo.
Dabi'u Rabiu sakataren alhazan jihar Kano yace yanzu ma sun fara shirin aikin hajjin badi domin duk wanda ya rigaka barci zai rigaka tashi. A jihar Kano haka suke aikinsu. Basa sako-sako da duk wani aikin da aka basu amana akansa.
Kamfanonin jiragen Najeriya da wani na Saudi suke yin jigilar alhazan inda kamfanin Mark ke da yawan alhazai. Ibrahim Jami'u shi ne jami'in labarun kamfanin. Yace an basu alhazai dubu arba'in da dari hudu da tamanin da shida. Kana sun kai doki ga wasu alhazai har ma da na kasashen waje. Misali sun kai alhazan kasar Niger su dubu biyar da yin zirga-zirga zuwa kasar sau tara.
Shugabannin hukumar alhazan Najeriya da aka kafa shekarar 2007 karkashin Muhammed Musa Bello zasu kammala aiki bayan shekara takwas domin shigowar sabbi. Salisu Shinkafi shi ne kwamishana mai kula da arewa maso yamma yace wanzuwar hukumar zai kara daidaita aikin hajjin Najeriya daidai da na zamani.
Yace an kai wani matsayi yanzu inda ba sai an shirya bikin ranar tashi ba. Yanzu da mutum ya duba kwamputarsa zai ga ranar da zai tashi da lokacin tashi. Nan take mutum zai san lambar dakinsa da lambar motar da zata daukeshi. Ynzu aikin hajjin yana gyaruwa. Aikin ya tashi daga na gargajiya ya dawo na zamani.
Bana dai alhazan Najeriya talatin ne suka rasa ransu yayin aikin hajjin sakamakon yawan shekaru da hawan jini. Cikin wadanda suka rasu har da wani sanannen malami daga Gombe Muhammed Basakkwace.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.