Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da kafa wata tawagar gwamnatin tarayya, wacce za ta tattauna da kamfanin Twitter da gwamnati ta dakatar da amfani da shi a kasar.
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohamed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ta hannun mai taimaka masa a fannin yada labarai, Segun Adeyemi.
“A cikin tawagar akwai babban Atoni-Janar din kasa kuma Ministan Shari’a, Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta yanar gizo, Ministan harkokin kasashen waje, Ministan ayyuka da samar da gidaje, ministan kwadago da sauran ma’aikatu.” Sanarwar ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa, bayan da Najeriya ta dakatar da ayyukan Twitter, saboda abin da ta kira barazanar da kamfanin ke yi na kasancewar kasar a matsayin kasa mai zama a dunkule, Twitter ya rubutawa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wasika, inda ya nuna shirinsa na sasantawa da gwamnatin tarayya.
Karin bayani akan: Twitter, IPOB, Shugaba Muhammadu Buhari, Lai Mohamed, Nigeria, da Najeriya.
A farkon watan nan na Yuni Najeriya ta haramta amfani da kafar ta twitter, bayan da kamfanin ya goge wani sako da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa, saboda a cewar kamfanin, ya sabawa ka’idojinsa da suka haramta wallafa kalamai masu tunzurarwa.
A sakon da Buhari ya wallafa, ya yi gargadi ne ga ‘yan IPOB da ke ta da kayar baya a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda ya ce zai tafiyar da su da irin yaren da suka fi fahimta, kalaman da Twitter ya ce ya sabawa ka’idojinsa.
A martanin da suka mayar, hukumoin kasar ta Najeriya sun dakatar da amfnai da shafin a daukacin kasar, tare da yin kira ga kamfanonin sadarwa da su toshe hanyoyin da za iya kai wa ga shafin na Twitter.
Sama da mutum miliyan 39 na amfani da shafin na Twitter a Najeriya, adadin da ya fi na kowacce kasa da ke nahiyar Afirka kamar yadda kididdigar baya-bayan nan ta nuna.