Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Ma'abota Twitter Ke Cewa Kan Goyon Bayan Da Trump Ya Nunawa Najeriya


Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

Biyo bayan jinjina da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa gwamnatin Najeriya don dakatar da kafar sadarwar Twitter, ma'abota amfani da kafar na bayyana ra'ayin mabanbanta.

Masu ra'ayoyi wadanda sun yi fice a lamuran yanar gizo a Najeriya na bugun jaki da taiki ne a lokaci guda sabanin wadanda ba su shahara ba da ke daukar kafar ta 'yan jari hujja ce.

Mai fafutuka Deji Adeyanju ya ce Twitter ta yi adalci wajen dakatar da shafin Donald Trump don haka ya ke murna in wata kasa ta dauki irin wannan mataki akan Twitter, kamar yadda Najeriya ta yi.

Shi ma ma'abocin yanar gizo dare da rana, George Onmonya Daniel da ke caccakar manufofin shugaba Bubari, ya ce bai yi mamakin matsayar da Donald Trump ya dauka ba.

Amma a na sa bangaren, mawallafin jaridar yanar gizo ta "Daily Nigerian" Jafaar Jaafar na ganin Trump ya yi daidai, kamar yadda shugaba Bubari ya takawa Twitter birki biyo bayan goge sakonsa da yake ganin mai ma'ana ne.

Ministan labarun Najeriya Lai Mohamed ya ce kamfanin Twitter ya fara tuntubar Najeriya don sanin mataki na gaba da za a dauka wajen sasanta wannan rikici.

Karin bayani akan: Twitter, Donald Trump, Shugaba Muhammadu Buhari, Lai Mohamed, Nigeria, da Najeriya.

Gwamnatin Najeriya a ta zargi dandalin wanda ke da mabiya sama da miliyan 39 a kasar, da ruruta wutar rikice-rikice a sassan kasar.

Kamfanin na Twitter ya haramta wallafa bayanai da ka iya ta da husuma ko nuna kyama ga wani ko wasu, ka’idar da ya ce Shugaba Muhammadu Buhar ya take.

Kusan mako guda kenan ana ta ka-ce-na-ce a Najeriya dangane da haramcin da hukumomin Najeriya suka saka wa kamfanin, matakin da ke shan suka a ciki da wajen kasar.

Hukumomin Najeriya sun ce matakin ya yi tasiri, yayin da wasu ke nuna akasin hakan, lura da cewa wasu na iya amfani da kafar VPN wajen shiga shafin.

Saurare cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG