Tsohon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Alhaji Bamanga Tukur ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba zai iya shawo kan matsalolin kasar shi kadai ba.
A cewar Bamanga, dole ne sai kowa ya sa hannu a al’amuran gyara kasa kafin a iya magance kalubalen Najeriya.
“Mutum shi kadai ba zai iya ba, Buhari ne zai nemi gona, Buhari ne zai yi kasuwa ya sayar ya kawo rahusa, to dole kowa ya zamana yana ciki.” In ji Bamanga.
Bamanga na magana ne yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilin Muryar Amurka Saleh Shehu Ashaka a Abuja.
A cewar Bamanga, “muddin ba ka bi liman ba (a sallah) ai ba jam’i.”
Dangane da batun masu kiraye-kirayen a raba kasa, tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP ya ce raba Najeriya ba shi ne mafita ba.
“Duk mai son kasar nan, yana son ta a hade, shi mai so a raba, in an ba shi, mai zai yi wanda ya wuce abin da ake yi yanzu.
“A kasar nan akwai inda za ka je ka shiga kasuwa ba ka ga Igbo, ko Bayerabe ko Bahaushe?
Dangane da batun matsaloli na tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta Bamaga ya ce abu uku ne za su iya magance wannan matsala.
“A yi karatu, a yi noma, a yi kasuwanci,” shi ne mafita ga Najeriya.
Sai dai ya ce duk wadannan abubuwa ba za su samu ba idan ba a magance matsalar tsaro ba.
“Wai yanzu kana jin tsoro ka taso daga Abuja ka je Kaduna, shin mai sayar da abu a Kaduna, da kai mai saye a anan (Abuja) zai yi wu?
Saurari cikakkiyar hirar: