Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana 'yan fashin dajin da suka addabi yankunan arewacin kasar a matsayin 'yan ta'adda.
Wannan batu na zuwa ne, a yayin zaman majalisar ta yi a ranar Laraba, inda 'yan majalisar su ka bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dukkan shugabannin yan’ fashi da makami wadanda ake nema ruwa a jallo a matsayin yan ta’adda tare da nemo su a duk inda suke da kuma gurfanar da su.
Matsayar haka ta biyo bayan kudirin da sanata mai wakiltar Sokoto ta Gabas, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir, da wasu takwarorinsa takwas suka gabatar.
Sanata Gobir ya koka da cewa yankin mazabarsa ta zama mafakar 'yan fashi da ke tserewa daga farmakin da ake yi musu a jihar Zamfara.
Inda ya bayyana cewa ko a ranar Asabar da ta gabata an kashe jami’an tsaro 21 a karamar hukumar Dama da Gangara yayin wata arangama da yan’fashi da ya kai ga mutuwar fararen hula da dama da kuma garkuwa da wasu da aba san adadinsu ba.
Gobir ya jaddada girman matsalar a matsayin lamarin da ya kai a ayyana yaki kan yan’fashin
Ya kuma bayyana takaicinsa kan yanda Najeriya ke asarar jami’an tsaro da dama wadanda aka horar da su a hannun yan fashin, lamarin da ya ce zai kawo hadari ga tsarin tsaron kasar idan ba a yi maganin sa ba.
Jihar zamfara dai ta yi kaurin suna wajen fuskantar ayyukan yan’ fashin da makami, sai dai a yanzu karfin iko da ayyukan sojin kasar daga jibge a jihar na tilastawa yan’fashin tserewa daga jihar zuwa kananan hukumomi na sabon birni da Isa dake Jihar Sokoto.
'Yan Majalisar sun bukaci gwamnati da ta yi dukkan mai yiwa tare da tabbatar da an kawo karshen hare haren da yan fashin ke kai wa al’umma da ba su ji ba, ba su kuma gani ba.