Femi Adeshina dai ya yi shelar cewa akasarin ‘yan Najeriya da ke caccakar shugaba Buhari a fili kan ziyarce shi a fadarsa na Aso Rock su ci abinci da shi kamar ba su yi ba.
Adeshina ya bayyana hakan ne a bayaninsa kan sauya shekar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode, wanda ya saba yiwa shugaba Buhari da jam’iyyar APC mai mulki munanan suka a shafinsa na mako-mako inda ya saba wallafa abubuwa.
A cewar Adeshina, shekara shida da watanni da ya kwashe ya na aiki tare da shugaba Buhari, ya ga irin karamci da yafiya da ya ke wa mutane ko da masu sukarsa ne kuma abin yana ba shi mamaki.
Adeshina ya ce, sau da yawa idan ya kai ziyara gidan Buhari musamman da yamma, ya na tarar da shi shuagaban yana cin abinci tare da mutanen da ko a ranar sun ci mutuncinsa da na kakanninsa a kafaffen yada labarai duk kuwa da zarginsa da riko da ake yi.
Yadda shugaban kasar ya karbi Femi Fani-Kayode a cewar Adeshina ya karyata masu ikirarin cewa Buhari ba shi da yafiya.
Idan ana bibiyan kafaffen yada labarai da na sada zumunta, Fani-Kayode ya yi kaurin suna a wajen sukar shugaba Buhari.
Tun bayan sauya shekar FFK zuwa APC da kuma kai shi fadar shugaban kasa inda ya gana da Buhari da shugaban rikon jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya yi ne yan Najeriya musamman wasu daga cikin jam’iyyar PDP da ya baro da kuma jam’iyyar APC da ya koma na ci gaba da sukarsa cewa bai da kima da mutunci.
A cikin kalamansa na baya wadanda ake ta yayatawa a kafaffen sada zumunta har da wanda Fani-Kayode ya yi wa dan shugaba Buhari, Yusuf Buhari fatar mutuwa bayan ya yi hatsari a kan babur kirar powerbike.
Adeshina ya kara da cewa banda Fani-Kayode, shugaba Buhari ya sha karbar bakuncin mutanen da ke sukar sa tare da cin mutuncinsa a fili tare ci abinci tare da su kan teburi daya.