Bincike ya nuna cewar jihohin kasar talatin da biyar ne suka karbi wadannan basussuka na kimanin Naira biliyan dari biyu da goma sha hudu in banda jihar Legas, wanda hakan ke nufin cewa jihohin da suka karbi tallafin akalla kowace ana tsammanin za ta biya Naira biliyan goma sha bakwai da miliyan dubu dari biyar.
Wannan yunkurin karbo kudaden ya biyo bayan kafa kwamiti ne da gwamnatin tarayyar kasar ta yi domin bin diddigin yadda gwamnonin suka yi amfani da kudaden tallafin, inda kwamitin ya gano cewa wasu jihohin sun yi amfani da kudaden bisa manufa a yayin da wasu jihohin kuwa su ka yi amfani da kudaden don kashe gararin gabansu.
Gwamnan Bauchi, Senata Bala Muhammed Abdulkadir (Kauran Bauchi) ya bayyana cewa wannan matsala ce.
Sai dai kuma a wani tsokaci masanin tattalin arziki kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago kwamred Abdullahi Koli ya ce fara biyan bashin a yanzu zai maida hannun agogo baya musamman ga batun biyan albashi a jihohi.
Ga dai rahoton Abdulwahab Mohammed a kan wannan batu:
Facebook Forum