Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Zata Rage Haraji Akan Kayan Masarufi Daga Najeriya


Shugaban Kasar Najeriya Mai Jiran Gado Muhammadu Buhari da MInistan Birtaniya David Cameron, Mayu 23, 2015.
Shugaban Kasar Najeriya Mai Jiran Gado Muhammadu Buhari da MInistan Birtaniya David Cameron, Mayu 23, 2015.

Birtaniya ta sanar da cewa a shirye take ta rage haraji da take daurawa akan kayayyakin da ake shigo da su daga Nigeriya da wasu kasashe masu tasowa.

Wata sanarwar da ofishin jakadancin Birtaniya dake Abuja ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne da zummar farfado da ka’idojin cinikayya, ceto sana’o’i da miliyoyin kudaden pounds da masu amfani da kayyayakin suke biya a kowace shekara.

Wannan ya biyo bayan sabon shirin cinikayyar kasar da kasashe masu tasowa tun bayan ficewarta daga Kungiyar Tarayyar Turai wanda ya shafi akalla kasashe 60, shirin da ake sa ran zai fara aiki daga jiya.

Wannan shirin zai cire ko kuma rage haraji kana ya saukaka sharudan cinikayya wanda zai bada dama a samu karin kayayyakin da zasu samu shiga, lamarin da zai samar da Karin sassauci fiye da yadda ya kasance a tsarin EU wanda Birtaniyya ta kasance mamabanta a baya.

Nigel Huddleston UK Minister forTrade
Nigel Huddleston UK Minister forTrade

Wani bangaren sanarwar ya ce “sama da kaso 99% na kayyayakin da ake shigo da su daga Najeriya kai tsaye za a iya shigo da su kyauta zuwa Birtaniya. Za a baiwa Najeriya Karin fifiko akan kusan kayayaki 3,000 da take shigo da su kasar. Alal misali, an cire kaso 4.5 daga nikaken cocoa, kaso 26.5 daga duk wani tatatsen lemu na juice, sannan kaso 14% daga tumatirin gwangwani."

Ministan ma'aikatar cinnikayyar kasashe Nigel Huddleston ne ya kaddamar da wannan tsarin a yayin wata ziyarar aiki da ya kai cibiyar kasuwancin Ethiopia mafi girma dake Bole Lemi.

"Ya ce wannan zai haifar da wasu damarmaki na cinikayya a fadin duniya wanda zai tallafawa rayuwar mutane, ya samar da ayyukan yi, sannan ya fadada cinikayyar kayan da aka sarafa a gida da kuma wanda aka sarafa domin sayarwa a fadin duniya. Zai kuma yi tasiri a harkar cinikayyar kasuwacin Birtaniya da masu amfani da wadannan kayan masarufi ta hanyar rage farashin kayayyaki da dama."

XS
SM
MD
LG