A yau aka kada kuri’a a Birtaniya, a wani zabe da sakamakonsa, zai samar da maslahar da aka jima ana jira, a yunkurin da kasar ke yi na ficewa daga kungiyar tarayyar turai.
Tun a shekarar 2016 al’umar kasar ta amince da wannan shiri bayan wani zaben raba-gardama da aka yi a shekarar 2016.
Kamfen din da Firai Ministan Boris Johnson, ya sa a gaba, ya mayar da hankalinsa ne kan taken “Get Brexit Done” – wato – mu tabbatar da yiwuwar ficewar Birtaniya daga tarayyar ta turai.
Johnson na kuma fatan idan jam’iyyarsa ta Conservative ta samu rinjaye a majalisar wakilan kasar, hakan zai ba shi damar sake gabatar da wani tsari da majalisar ta yi fatali da shi a baya, kan yadda Birtaniyar za ta fice daga kungiyar ta EU.
Kokarin da Firai ministan ke yi shi ne, ya ga ya cimma wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da aka shata kasar za ta fice daga tarayyar.
Facebook Forum