Likitoci a Najeriya na ci gaba da yin gargadin cewa muddin aka yi sako-sako da yadda ake tunkarar annobar cutar COVID-9, to hadarin dake tattare da hakan ba kadan bane.
Jagorar gidauniyar kiwon lafiya ta “Medicaid Foundation” Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta ce bayan yakin da hukumomi ke yi don shawo kan wannan annoba, suma jama'a dole ne su dauki matakin da zai karfafa kokarin gwamnati.
Dr. Zainab Bagudu ta kuma ce yana da muhimmanci jama'a su kiyaye abubuwan dake kara baza yaduwar cutar musamman kiyaye ka'idojin kiwon lafiya da kuma kula da fadakarwar da malaman kiwon lafiya ke yi. Ta kara da cewa a kasar China inda cutar ta samo asali, bin ka'idoji da kuma bin umurnin jami'ai ya taimaka wajen shawo kan cutar.
A kasashen Turai kamar Italiya inda wasu suka yi watsi da matakan da ya kamata a bi, yin hakan ya tsananta lamarin sosai har rayuka da yawa suka salwanta. Dr. Zainab ta yi fatan lamarin ba zai faru ba a Najeriya, muddin mutane suka yi abin da yakamata.
Tsohon shugaban hukumar yaki da cututtuka a Najeriya, Farfesa Abdulsalam Nasidi, ya ce abin takaici ne ganin har yanzu wasu ‘yan arewa basu ma amince cewa akwai cutar ba. Ya kuma ce babban aikin dake gaban gwamnatoci shine a shiga gangamin wayar da kai da yin fadakarwa ka'in da na'in don ankarar da jama'a.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum