A cewar hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, akwai akalla ‘yan gudun hijira miliyan 65.3 a duk fadin duniya.
Kiyasi ya kuma nuna cewa a kullum, ‘yan gudun hijira dubu 42,500 suke ficewa daga gidajensu domin neman mafaka.
Kuma bayanai sun nuna cewa rikicin Syria shi ne rikici mafi muni da ya fi samar da ‘yan gudun hijira inda mutane miliyan 11 suka bar kasar, wanda hakan shi ne kashi 45 na al’umar kasar.
A Najeriya, rikicin Boko Haram dake faruwa a arewa maso gabashin kasar ya tarwatsa sama da mutane miliyan guda inda rayuka da dama kuma suka salwanta.
A shekarar 2001, Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 20 ga watan Yuni a matsayin ranar ‘yan gudun hijira.
Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu ya ziyarci wasu daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijirar dake Maiduguri a jihar Borno domin jin halin da su ke ciki:
Facebook Forum