Uwargidan Gwamnan tayi wannan alkawarin ne lokacin da take rabon kayayakin abinci ga nakasassu dake garin Maiduguri.
Hajiya Nana Shettima tace tasan irin halin da irin wadannan nakassu ke ciki musammam ma a wannan yanayi da al’ummar jihar Bornon suka samu kansu ciki. Amma tace suci gaba da hankuri, domin zasu ci gaba da ganin sun tallafa musu ta wurin harkokin karatun su dama sama musu sanao’i.
Tace an san cewa suna hankuri da yanayin da dukkan mu muka tsinci kanmu, a gaskiya zamu yi iya gwargwadon karfin mu, mu tallafa, musammam ku nakasassu, don ALLAH ‘Yan uwa ayi hankuri.’’
Hajiya Amma Abubakar ita ce babban Sakatariyar maaikatar mata na jihar Borno kuma tayi karin haske akan gudunmowar da suka bayar.
Tace mai girma matan gwamna, daman karkasahin kulawar gidauniyar data kafa, ta sha bada tallafi ga kungiyoyi da yawa amma na wannan karon ta baiwa nakasassu ne, a cikin su akwai guragu, akwai makafi, akwai kurame, da kuma kutare. Ta basu shinkafa buhu dari biyu, Sugar 200, ta kuma basu hatsi buhu 50, da kuma masara buhu 50.’’da kuma kudi dubu dari biyar, sabo da su shiga mota domin komawa gidajen su’’
Ga Haruna Dauda Biu da Karin bayan
Facebook Forum