Bayanan da hukumar kididdiga ta NBS ta fitar ne suka nuna cewa, kudaden shiga da kasar ke samu na cikin gida sun karu da kashi 0.11 a zangon karshe na shekarar 2020.
“Wannan shi ne haske na farko na karuwar tattalin arzikin kasar da aka gani cikin watanni uku na karshen na shekarar 2020’” a cewar bayanan da hukumar ta NBS ta fitar, wadanda aka wallafa a shafin Twitter hukumar.
Tun dai bayan da annobar coronavirus ta bulla, farashin mai ya fadi a bara, Najeriya ta fada cikin komadar tattalin arziki a kwata na uku na shekarar 2020, wato a karo na biyu cikin shekara hudu.
A baya dai hukumomin kasar sun yi hasashen cewa sai a zangon watanni uku na farko na shekarar 2021 tattalin arzikin kasar zai farfado.
Amma sabbin kididdigar da aka yi, sun nuna cewa an samu sammakon farfadowar tattalin arzikin na Najeriyar wacce ta fi kowacce kasa yawan al’uma a nahiyar Afirka.
Babban abin da ya haifar da bunkasar tattalin arzikin a cewar hukumar ta NBS shi ne, yadda aka maido da harkokin kasuwanci bayan da aka sassauta matakan da aka saka na dakile yaduwar coronavirus.