Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Bayyana Kudurin Tsagaita Bude Wuta A Gaza Ba Da Amincewar Netanyahu Ba


Biden - Netanyahu
Biden - Netanyahu

A lokacin da shugaba Biden ya fito fili ya bayyana kudurin tsagaita bude wuta a Gaza, da Isra'ila da Amurka suka shirya kuma suka aikewa kungiyar Hamas, ya bayyana hakan ne ba tare da neman amincewar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba, in ji wasu jami'an Amurka uku masu masaniya kan lamarin

WASHINGTON, D. C. - Jami’ai sun ce, da gangan Amurka ta yanke shawarar yin gaban kanta ta sanar da shirin- wani mataki na ba saban ba da abokan kawancenta na kut-da-kut, abinda zai takaita damar da Isra'ila ko Hamas ke da ita na ficewa daga yarjejeniyar.

"Ba mu nemi izinin sanar da shawarar ba," in ji wani babban jami'in Amurka, wanda aka sakaya sunansa wanda ya ke da ‘yancin yin magana game da tattaunawar.

"Mun sanar kawai da Isra'ilawa cewa za mu yi jawabi ne kan halin da ake ciki a Gaza, ba mu yi cikakken bayani kan ko menene ba."

Masu shiga tsakani daga kasashen Amurka, Masar da Qatar sun dauki watanni suna kokarin shiga tsakani don kawo karshen rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatan mutane, amma aka kasa cimma yarjejeniyar.

Sanarwar da Biden ya bayar da kuma gabatar da ita a matsayin tayin da "Isra'ila ta yi ," an yi shi ne da fatar zai kai ga tsagaita wuta da kuma matsa wa Netanyahu lamba, in ji Jeremi Suri, farfesa a tarihi da al'amuran jama'a a Jami'ar Austin ta jihar Texas.

Suri ya ce "Biden yana kokarin matsawa Netanyahu lamba ne domin ya amince da wannan kudiri." Da aka tambaye shi ko sanarwar ta Biden wani yunkuri ne na matsin lamba kan Netanyahu, wani jami'in Isra'ila ya ce babu wanda zai iya hana Isra'ila murkushe Hamas da karya lagon ta.

Jami'in da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "Tsarin cewa matsin lamba zai sa Isra'ila ta yi sabanin ra'ayinta na kasa, wauta ce." "Hamas ya kamata a matsa wa lamba."

Da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, mai magana da yawun kwamitin tsaron kasar Amurka John Kirby ya musanta cewa gwamnatin kasar na kokarin yi wa shugaban na Isra'ila zagon kasa ne.

To sai dai Shugaban Hamas ya ce a ranar Laraba kungiyar za ta bukaci kawo karshen yakin Gaza na din-din-din ne da kuma janyewar Isra'ila a wani bangare na shirin tsagaita bude wuta, wanda hakan na nuna kawo cikas ga kudirin sulhun da shugaban Amurka Joe Biden ya yi tsokaci a makon jiya.

A daya bangaren kuma Isra'ila ta ce ba za a dakatar da fada a lokacin tattaunawar tsagaita bude wuta ba, ta kuma kaddamar da wani sabon hari a tsakiyar yankin zirin Gaza da ke kusa da birni na karshe wanda har yanzu tankokin nata ba su kai farmaki ba.

Ba a dai bayyana ko wannan sabon shirin tsagaita bude wutan zai yi nasara ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG