Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Sa Ran Isra'ila Za Ta Amince Da Shirin Tsagaita Wuta Idan Hamas Ta Yarda Da Shi


Israeli firefighters put out flames in a field after rockets launched from southern Lebanon landed on the outskirts of Katzrin in the Israel-annexed Golan Heights on June 2, 2024.
Israeli firefighters put out flames in a field after rockets launched from southern Lebanon landed on the outskirts of Katzrin in the Israel-annexed Golan Heights on June 2, 2024.

Idan har Hamas ta amince da shirin tsagaita wuta da Isra'ila ta fitar a Gaza, Amurka na sa ran Isra'ila za ta amince da shirin, in ji kakakin fadar White House John Kirby a ranar Lahadi.

"Wannan shawara ce ta Isra'ila. Muna da kyakkyawan fata cewa idan Hamas ta amince da shawarar - kamar yadda muka aika musu, shawarar ta Isra'ila - to itama Isra'ila za ta yi na’am," in ji Kirby a cikin wata hira da shirin ABC News na "This Week".

Masu shiga tsakani na zaman lafiya daga Masar da Qatar da kuma Amurka sun yi kira ga bangarorin biyu da su amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin wadanda ake garkuwa da su da shirin shugaban Amurka Joe Biden ya zayyana jiya Juma'a.

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, ya fada a ranar Lahadi cewa, Isra'ila ba za ta amince da Hamas ta ci gaba da mulkin Gaza a kowane mataki yayin shirin zaman lafiyar, kuma tana nazarin wasu hanyoyin da kungiyar ta Islama za ta dauka.

A cikin wata sanarwa da Gallant ya fitar, ya ce "Yayin da muke gudanar da muhimman ayyukan soji, hukumar tsaro a lokaci guda zata tantance wata hanyar mulkin Gaza da zata maye gurbin Hamas."

Gallant ya ce "Za mu kebe yankuna a Gaza, mu kawar da mayakan Hamas daga wadannan yankuna da kuma gabatar da dakarun da za su kafa gwamnati da za ta maye gurbin Hamas - madadin da ke barazana ga Hamas," in ji Gallant.

Gallant bai yi karin haske kan wasu hanyoyin da za a iya bi ba.

Ana sa ran majalisar ministocin yakin Isra'ila, wadda Gallant mamba ne a majalisar, za ta yi zama a yau, kamar yadda kafafen yada labarai na Isra'ila suka ruwaito, bayan da shugaba Biden ya gabatar da wani tsarin da zai kai ga kawo karshen yakin Gaza.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Asabar cewa "Sharudan Isra'ila na kawo karshen yakin bai canza ba: wargaza mayakan Hamas da karfin mulki, kubutar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma tabbatar da cewa Gaza ta daina zama barazana ga Isra'ila."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG