Dan wasan tsakiya na kasar Denmark da ya yanke jiki ya fadi yayin wani wasa Christian Eriksen ya fito daga asibiti.
An sallamo Eriksen dan shekara 29 a ranar Asabar kamar yadda hukumar kwallon kafar kasar ta bayyana a shafinta na Twitter.
Dan shekara 29, Eriksen ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da suke karawa da Finland a gasar cin kofin turai ta 2020 da ke wakana a sassan nahiyar a ranar 13 ga watan Yuni.
An garzaya da shi asibiti bayan da ma’aikatan lafiya suka farfado da shi, inda aka ayyana cewa ya samu matsalar bugun zuciya ne.
Rahotanni sun ce bayan da aka sallame shi a asbiti, Eriksen wanda ke bugawa Inter Milan wasa a Italiya, ya kai wa abokanan wasansa ziyara inda daga baya kuma ya tafi gida wajen iyalinsa.
Finland ta lallasa Denmark da ci 1-0 a wasan.
Dole sai Denmark ta lashe was anta da Rasha da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni, idan har tana son ta shiga Zangon ‘yan 16 a gasar.
Euro 2020: Magoya baya suna ta murna bayan Denmark ta lalasa Rasha da ci 4-1 da ya kaita shiga rukuni na 16 a gasar kasashen Turai na 2020