Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Da 'Yan Tawayen Libya Sun Kashe Sojojin Chadi Shida


Soldiers of the Chad Army sit on the back of a Land Cruiser at the Koundoul market, 25 km from N'Djamena, on Jan. 3, 2020, upon their return after a months-long mission fighting Boko Haram in Nigeria.
Soldiers of the Chad Army sit on the back of a Land Cruiser at the Koundoul market, 25 km from N'Djamena, on Jan. 3, 2020, upon their return after a months-long mission fighting Boko Haram in Nigeria.

Sojojin kasar Chadi 6 aka kashe a kusa da kan iyakar Libya da kuma kudancin yankin Tafkin Chadi, inda mayakan kungiyar Boko Haram su ke kai hare-hare, a cewar wasu jami’ai biyu. 

Gwamnan lardin Tibesti, Ali Maide Kebir, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa – AFP, cewa a ranar Juma’a “wasu ‘yan bindiga 3 sun yi kwanton bauna wa wata motar jami’an soji a Kouri,” kusa da kan iyaka da kasar Libya mai fama da yaki, suka bude muta wuta inda suka kashe sojoji 3 tare da raunata wasu 2.

Sojojin Chadi a Tibesti suna fuskantar hare-hare daga ‘yan tawaye da kuma masu hakar zinari ba bisa ka’ida ba.

A yammacin yankin Tafkin Chadi da ke iyaka da Najeriya, Nijar da Kamaru, wata motar soji “ta taka wata nakiya da ‘yan Boko Haram suka dana, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 3 da raunata wasu 8,” a cewar Mahamat Seitchimi, wani babban jami’in kasar.

Kamfanin dillancin labaran na AFP ya yi kokarin jin ta bakin gwamnatin kasar Chadi, to amma ba ta tabbatar da mutuwar sojojin ba.

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekara ta 2009, sun kashe fiye da mutane 36,000, kana kuma suka raba iyalai fiye da miliyan biyu da muhallansu.

Tuni kuma da tashin hankalin ya bazu zuwa kasashen Nijar, Kamaru da Chadi.

A watan Maris dakarun kasar Chadi sun yi asara mafi yawa a rana daya, sa’adda aka yi wa sojojinsu 98 kisan kiyashi a sansaninsu da ke Bohoma, a gabar tafkin Chadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG