Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadji: 'Yar Nijar A Cibiyar Sama Jannatin Amurka


Dr Fadji Maina
Dr Fadji Maina

Wata matsashiya ‘yar jamhuriyar Nijer, Dr Fadji Maina da ta karanci fannin kimiyar Sammai da Duniyar da ake ciki ta soma aiki a ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Amurka wato NASA a farkon watan nan na Satumba.

Wannan shi ne karon farko da wani dan Nijer ke shiga sahun kwararrun jami’an NASA abinda ya sa Shugaba Issouhou Mahamadou ya kira Dr Fadji Maina ta wayar tarho ya jaddada mata goyon bayan baki dayan al’ummar wannan kasa. Kan haka ne wakilin Sashen Hausa, Souley Moumouni Barma ya yi hira da Minstan Raya Al’adu, Alhaji Assoumana Malan Issa, wanda ya ce ma’aikatar da Dr Fadji ke aiki yanzu shahararriya ce a duniya ba ma Amurka kawai ba.

NASA mars2020 perseverence rover and helicopter
NASA mars2020 perseverence rover and helicopter

Wata Na'urar NASA a Watar Duniyar

Minista Assoumana ya ce ga ‘yan Nijar abun farin ciki ne da matukar alfahari a ce a halin yanzu har an samu wani dan kasar da ke aiki a wata shahararriyar ma’aikatar kimiyyar Amurka. Ya ce abubuwan da ke bada sha’ari game wannan cigaban shi ne cewa mace ce ta yi wannan abin yabon kuma matashiya. Y ace duk wani dan Nijar da murna da hakan kuma ana ma ta fatan Allah ya kara ma ta hikima da hazaka.

Da aka tambayi Ministan abin da Shugaban Nijar Issouhou Mahammadou ya gaya wa Dakta Fadji lokacin da ya kira ta a wayar tarho, sai y ace Shugaban kasa ya jinjina ma ta kuma ya fi kowa farin cikin abin da ya faru, inda Dakta Fadji ta daukaka sunan Janhuriyar Nijar. Ya ce duk lokacin da ta nemi wani goyon baya kasar Nijar za ta ba ta; kuma akwai wani kwamiti na tantancewa da kuma kiran ‘yan Nijar da su ka yi fice ta fannoni daban daban. Nan gaba kwamitin zai gayyaci Dakta Fadji ta gana da Shugaban kasa.

Ga Suleiman Barma da cikakken rahoton:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG