Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barayin Shanu Sun Addabi Wasu Kauyuka a Jihar Zamfara


Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Gaggawa a Zamfara
Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Gaggawa a Zamfara

Kwanaki hudu kenan wasu barayin shanu a jihar Zamfara ke addabar wasu kauyuka da suka kai goma, wanda hakan yayi sanadiyar raba dubban mazauna kauyukan da gidajensu.

Rahotanni sun nuna cewa har ya zuwa yanzu ‘yan bindigar suna nan suna ci gaba da kai hare-hare, musamman a yankunan kananan hukumomin Mulki da Tsafe da Gusau, lamarin da ya sa dubban mazauna kauyukan barin gidajensu domin gudun hijira.

Wani da ya nemi a boye sunansa mazaunin garin Mada a karamar hukumar Gusau, ya ce yanzu haka barayin shanun sun addabi mutanen yakin suna cin karensu babu babbaka, wanda yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira sama da dubu uku a garin Mada duk a dalilin wannan tashin hankalin.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijira a wata makaraman firame ta garin Mada sun bayyanawa Muryar Amurka irin halin da suke ciki. Inda wata mai suna Maimuna ta ce an kore musu shanunsu babu adadi, kuma an kashe musu ‘yan uwa.

‘Yan jihar da yawa dai na ganin halin da ake ciki a Zamfara ya yi tsanani, a daidai lokacin da kuma suke zargin gwamnatin tarayya da kafafen yada labarai da yiwa lamarin rikon sakainar kashi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai ana ci gaba da samun kwararar mutane dake kaura daga gidajensu, suna kuma tsugunnnar da kansu a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira, duk da yake suna korafin samun tallafi ko kuma kulawa da gwamnatin jihar.

Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG