Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kwato karin wasu daliban sakandaren gwamantin tarayya da ‘yan bindida suka sace a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar.
"Dakarun Najeriya da ke aiki karkashin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ tare da hadin gwiwar dakarun saman Najeriya, sun kubutar da karin wasu daga cikin daliban FGC birnin Yawuri." wata sanarwa da dakarun Najeriya dauke da sa hannun Darektan yada labarai Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ta ce.
"An kubutar da malami daya da dalibai uku a yankin Makuku, sannan sojoji sun kashe dan bindiga daya sun kuma kwato babura tara da wayoyin hannu hudu daga ‘yan bindigar da ke tserewa."
Karin bayani akan: Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, jihar Kebbi, daliban, ‘yan bindiga, sojojin, Nigeria, da Najeriya.
Sanarwar ta Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ta kara da cewa, an tura karin dakaru zuwa yankin "don su mamaye dajin, su kuma hana ‘yan bindigar sakat."
A ranar Alhamis ‘yan bindiga suka far wa makarantar sakandaren da ke Yauri suka yi awoan gaba da dalibai da dama, wadanda wasu rahotanni ke cewa adadinsu ya kai 80.
Kwana guda bayan satar daliban, sojojin sun kubutar da malamai biyu da dalibai biyar.