Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Ba Za A Yi Amfani Da Karfin Bindiga Ba A Kokarin Ceto Daliban Kebbi – Sanata Aleiro


Sanata Adamu Aleiro (Facebook/Aleiro We Follow)
Sanata Adamu Aleiro (Facebook/Aleiro We Follow)

Mafi akasarin 'yan sandan Najeriya na wajen gadin ministoci, gwamnoni, sanatoci da manyan ma'aikatan gwamnati, in ji Aleiro.

Tsohon gwamnan jihar Kebbi Sanata Muhammad Adamu Aleiro ya ce jami’an tsaro a matakai daban-daban na iya bakin kokarinsu wajen ganin sun kubutar da daliban sakandaren tarayya na Yawuri da aka sace kusan mako biyu da suka gabata.

A ranar 17 ga watan Yunin, ‘yan bindigar suka kutsa kai cikin makarantar suka yi awon gaba da dalibai da malamai.

Rahotannin sun ce sun kashe daya daga cikin jami’an tsaro da ke gadin makarantar a lokacin harin.

Wasu rahotanni sun ce an yi nasarar kubutar da wasu daga cikin daliban bayan da aka sace su.

Sai dai yayin da aka doshi mako biyu ba tare da an ji halin da sauran daliban ke ciki ba, Sanata Aleiro wanda ke wakiltar jihar ta Kebbi a majalisar dattawa ya ce hukumomin tsaro ba sa son su yi amfani da karfin bindiga wajen kubutar da daliban.

“Ka san idan irin akwai wannan lamari, ba za ka zo ka yi amfani da karfin bindiga ba, saboda idan ka yi amfani da karfin bindiga, ba za ka samu biyan bukatar fitar da yaran nan lafiya lau ba, karfin bindiga zai cutar da yaran nan.” Aleiro ya ce a zantawa ta musamman da ya yi da Muryar Amurka.

Wasu rahotanni sun ce kwanaki kadan bayan satar daliban, jami’an tsaron sun yi wa ‘yan bindigar kawanya, lamarin da ya ba da kwarin gwiwar za a kubutar da daliban, amma har yanzu abin ya ci tura.

Dangane da makomar ilimi a arewacin Najeriya, duba da yadda mahara suka addabi yankin arewacin Najeriya, Aleiro wanda ya mulki jihar ta Kebbi tsakanin 1999 zuwa 2007 ya ce, akwai matakan da ake dauka don magance wannan matsala.

“Akwai abubuwa da muke yi da dama musamman karfafa jami’an tsaro, mun lura cewa jami’an tsaro sun yi kadan. ‘Yan sanda duka-duka abin da ke gare mu bai fi dubu 360 ba, kuma rabin ‘yan sandan nan suna wajen aikin gadi na gidajen ministoci, gwamnoni, sanatoci, da manya-manyan ma’aikatan gwamnati.

“Ka ga abin kawai da yage 180 ne, kuma bai isa ya ba da tsaro ga mutum miliyan 200 na Najeriya ba.”

Saurari cikakkiyar hirar Sanata Adamu Aleiro tare da Murtala Faruk Sanyinna:

Dalilin Da Ya Sa Ba Ma So A Yi Amfani Da Karfin Bindiga A Kokarin Ceto Daliban Kebbi – Sanata Aleiro - 3'24"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00


XS
SM
MD
LG