Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 136 Afuwa


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Albarkacin murnar bikin babban sallah na bana da al'ummar Musulmi suka gunadar a ranar Talata, Gwamnar Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 136 afuwa daga kurkukun jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba kowanne daga cikin fursunonin da aka yi wa afuwa Naira dubu biyar a matsayin kudin da zai mayar da su gidajensu da kuma kyautar shanu da raguna don gudanar da bikin sallah.

A cewar sanarwar da Babban Sakataren yada labaru na Jihar Malam Abba Anwar ya fitar, shawarar ta biyo bayan ziyarar da gwamnar ya kai gidan fursunoni dake Goron – Duste a Ranar Sallah

"Ku 'yan Najeriya ne wadanda suka cancanci a kula da su dalilin da ya sa mu ka kawo muku ziyara a yau kenan don gudanar zagayowar bikin babbar sallah ta hanyar yin afuwa ga wasunku," in ji Ganduje

Gwamnar ya kuma bukaci yan’tantun fursunonin da su yi alkawari kan ba su sake komawa laifukan da suka aikata a baya ba

An dai yafe wa wadanda su shafe tsawon lokaci a tsare da kuma wadanda ke fama da jinya hada da wadanda suke tsare saboda kasa biyan tarar da aka yi musu, a cewar Anwar.

Wannan yunkuri ya biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na rage cunkoso fursunoni a gidajen kurkuku a duk fadin kasar, inda Ofishin kididdiga na kasa a shekarar 2017 ya fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa a jihar Kano kawai fursunonin da ke kurkuku sun haura dubu biyu.

XS
SM
MD
LG