Da yake bayani, Staffen ya ce "Ganin yadda wannan yarjejeniya ta kasashen yankin Atlantika, ke da muhimmanci ga Shugabar, a ganinta ya dace a yi magana ta gaskiya game da batun banbancin da ke tsakani yanzu," abin da mai magana da yawunta Steffen Seibert ya fada yau Litini a wani taron manema labarai kenan.
"Lokacin dogaro kan juna kusan ya wuce, kamar yadda na lura cikin 'yan kwanakin da su ka gabata," a cewar Merkel, a yayin da ta ke jawabi a wani yakin neman zabe a Bavaria.
Merkel, kamar wasu Shugabannin Turai, sun caccaki manufofin Shugaban Amurka Donald Trump, a taron G-7 da aka yi a Sicily, inda bai jaddada goyon bayansa ga batun yaki da dumamar yanayi kamar yadda aka amaince a Paris ba. A wata takardar sanarwar bayan taro, dukkannin kasashen G-7, in banda Amurka, sun kuduri aniyar yakar dumamar yanayi.
Facebook Forum