Firayim Ministan Nijar Briji Rafini yayi kira ga 'yan Nijar da suyi addu'o'i domin samun zaman lafiya dawamamiya albarkacin watar azumin Ramadan.
Ya bayana haka ne jim kadan bayan da majalisar koli ta malaman kasar ta bada sanarwar ganin watan azumin Ramadan.
Yana mai cewa kasar na bukatar addu’ar ‘yan kasa domin karuwar arzikin da zaman lafiya maidorewa da kuma samun damuna mai albarka.
A na sa bangaren daya daga cikin Malaman addinin Islaman kasar Malam Jihadi, yace dukkan ibadah da dan Adam ya aikata tashi ce , abin nufi shine duk abinda mutun ya aikata na aikin ibadah akwai abinda aka sheda a fili cewa shine sakamakon bawa, amma azumin watan Ramadan Allah ya boye sakamakon da zai baiwa mai azumi wannan tsakanin bawa da mahallincinsa ne.
A nasu bangaren ‘yan kasuwa sun ce farashin kayayyaki babu laifi sai dai akwai wasu kayayyakin da ba a samun su yanzu haka a kasuwanni in ji wani dan kasuwa me suna Malam Tasiu.
Jama’ar kasar ta Nijar, dai na ci gaba da nuna kyakkyawan fata game da sagayowan watan Azumin Ramadan.
Facebook Forum