A wani taron manema labari da kungiyar ta kira a birnin Legas, ta ce matakin karin dubban daloli da kanfanonin su ka yi wa Najeriya tamkar zagon kasa ne, a kokarin da kasar take na sake farfadowa daga illar cutar coronavirus, kamar sauran kasashen duniya.
Shugaban Majalisar Alhaji Bello, ya ce ba tare da an sanar da hukomomin Najeriya ko kungiyarsu ba, an kara haraji ga masu shigar da kwantenonin kayayyaki zuwa kasar, inda yanzu suke biyan karin dalar Amurka $1000 zuwa $1500, lamarin da ya ce ba za su lamunta ba.
Majalisar ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su tashe tsaye wajen shawo kan wannan matsala, domin kudaden harajin da kasar ke karba ya yi kasa, haka kuma farashin kayayyaki za su ci gaba da tashi.
Shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, Alhaji Abubakar Garba Umar, wanda ya halarci taron manema labaran, ya ce gwamnati na goyon bayan kungiyar na adawa da matakin karin harajin.
Yayin da kungiyar ta bayyana rashin amincewarta ta ce zata ci gaba da gabatar da kokenta ga hukumomin kula da hada-hadar kasuwanci na Teku da jiragen ruwa.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin daga Legas.
Facebook Forum