Tun lokacin da aka samu wata hatsaniya tsakanin ‘yan kungiyar Shi’a, da Sojoji ake ta fitar da bayanai daban daban dangane da musabbabin abunda ya faru da kuma irin hujjojin da suka gabata daya sanya rundunar Sojojin Najeriya suka dauki matakin da suka dauka.
Ganin cewa ‘yan kungiyar ta Shi’a, sunyi zarge zarge daban daban cewa an nuna masu fin karfi kuma ba’a bi ka’ida ba kan matakan da aka dauka akansu.
Kakakin rudunar Sojojin Najeriya Kanel Sani Usman Kukasheka, yace rundunar Sojojin Najeriya, bata da niyyar musgunawa wasu da suke bin wani addini ko wasu ‘yan kabilu.
Ya kara da cewa duk wani da yake tunani ko yake ganin cewa ana kuntatawa wasu to hakikanin gaskiya bai ma mutane adalci ba masamman Sojojin Najeriya, idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru kafin ranar da kuma ranar da kuma abubuwan da suka biyo baya.
Yana mai cewa abunda ya faru yana da nasaba da wasu abubuwa da suka faru kimanin shekara 6, da suka wuce, amma ba yadda za’a ayi ana ganin mutane su nemi su hallaka wasu ko kuma su nemi su yi banna a zura masu ido.