Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan shawarar da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yanke na dage zaben kasar da aka ayyana makon gobe da kwana uku. Majalisar tace wannan mataki ba koma baya bane ga kasar da take fama da matsaloli.
"A ganina gaskiya, ganin batun tsaro mai sarkakiya da kasar take fama da shi, yana da muhimmanci a yi zaben cikin yanayi mafi dacewa," kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric, ya fada a birnin New York.
Yace ofishin kiyaye zaman lafiya na majalisar, zai taimakawa kasar wajen raba katunan zabe, kuma zai agazawa dakarun kasar a bangaren tsaro.
Tun farko hukumomin kasar sun ayyana zaben shugaban kasa da na majalisar ranar Lahadi mai zuwa, yanzu an tura shi gaba zuwa ranar Laraba 30 ga watan nan na Disamba,bayan da jami'an kasar suka lura cewa suna bukatar karin lokaci.