Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov, ya fada yau Laraba cewa ‘yan tawaye a gabashin yankin Ghouta da ke Syria na toshe hanyar kai kayayyakin agaji, suna kuma hana mutane barin wurin.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da Rasha ta kira a tsagaita wuta domin kai taimakon agaji a farmakin da sojojinta ke kai wa.
Dama shirin na Rasha an yi shi ne da zummar tsagaita wuta na sa’oi biyar don mutane su sami taimako ko su fita daga yankin da ‘yan tawaye suka mamaye wanda dakarun gwamnati suka yi wa kawanya tun a 2013.
Kafafen yada labaran Syria sun zargi mayakan ‘yan adawa da hana fitar da mutane kwanaki biyu a jere.
Babu farar hular ko daya da ya iya fita ya zuwa yanzu, a yankin da ke da mutane kusan 400,000.
‘Yan tawaye sun yi watsi da zarge-zargen jiya Talata, ranar farko da aka fara tsagaita wutar, wanda ya sa bangarorin biyu dorawa juna laifi akan tashin hankalin da ke ci gaba da faruwa.
Kungiyar da ke kare hakkokin jama’ar Syria mai mazauni Brrtaniya ta ba da rahoton cewa an ci gaba da fada a gabashin Ghouta har zuwa yau Laraba.
Facebook Forum