Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben shugaban Nigeria na 2011


People's Democratic Party (PDP)
People's Democratic Party (PDP)

Shugaban PDP na kasa yace shugaba Jonathan nada cikakken ‘yancin tsayawa zaben shekara mai zuwa.

Madugun jam’iyyar dake kan karagar mulki a Nigeria yace shugaba Goodluck Jonathan nada cikakken ‘yancin tsayawa takara a zaben da za’a yi a shekara mai zuwa, duk kuwa da kiranye-kiranyen da wasu ke yi na cewa sai shugaba na gaba ya fito daga sashen arewancin kasar.

A ran Alhamis ne madugun jam’iyyar PDP, Okwesilize Nwodo yake wannan kalamin bayan da wata muhimmiyar kungiyar jagabannin Arewa tayi kira akan dukkan jam’iyyun siyasa na Nigeria da su tsaida ‘yan Arewa a matsayin ‘yan takaransu na shugaban kasa a zaben badi – wanda in anyi hakan, an kebance shi shugaba Jonathan ke nan a gefe.

A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta fito tana cewa wajibi ne akan dukkan jam’uiyyun siyasa su tsaida ‘yan Arewa don tabattarda adalci a tsakanin ‘yan kasar. A inda aka fiton nan dai, jam’iyyar PDP takan gudanarda mulkin karba-karba ne inda take raba mukamin shugaban kasa a tsakanin ‘yan kudu da ‘yan Arewa. A zaben 2007 ma dan Arewa kuma Musulmi da PDP ta tsaida, Umaru Musa ‘Yar’adua ne ya lashe zaben kuma, bayan mutuwarsa ne Goodluck Jonathan, dan Kudu kuma Kirista, ya dauki ragamar mulki. Har zuwa yanzu shi shugaba Jonathan bai fito yace zai tsaya takaran ba.

XS
SM
MD
LG