Hukumar zaben Nigeria ta bada sanarwar ranakkun da za’a gudanarda zabukkan shugaban kasa, gwamnoni da yankunan kananan hukumomi. Hukumar zaben tace a ran 21 ga watan Afrilun badi ne za’a gudanarda zaben shugaban kasa da na ‘yanmajalisun tarayya, amma zaben gwamnoni da na majalisun jihohi ne za’a fara yi a ran 14 ga watan na Afrilu. Shugaban hukumar zaben Maurice Iwu yace anyi tanadin gudanarda zabukkan raba gardama a cikin lokaci ta yadda za’a tabattarda cewa an rantsarda sabuwar gwamnati a ran 29 ga watan Mayu na badi. A cikin wannan watan na Mayu na badin ne shugaban Nigeria na yanzu Olusegun Obasanjo zai kamalla wa’adodinsa guda biyu. A farkon shekaran nan ne dai majalisun tarayya na Nigeria suka kashe yunkurin da akso yi na chanja kundin tsarin mulki don baiwa shugaba Obasanjo damar yin wa’adi na ukku.