A yayin wani taro na yini guda a Kano da kungiyar WRAPA mai rajin wayar da kan mutane game da hakkokin mata da iyali, da hadin gwiwan Cibiyar nazari da bincike kan bunkasar harkokin addinin Musulin da hulda da sauran addinai ta Jami’ar Bayero Kano suka shirya, an yi musayar ra’ayi kan hanyoyin bada kariya daga kalubalen da matan aure da ‘yammata ke fuskanta a sassan Najeriya.
Hajiya Saudatu Mahdi Shehu shugabar kungiyar WRAPA ta ce makasudin shirya taron shine shigo da shugabannin addinai dana al’umma da kuma masu rike da sarautu cikin harkokin yaki da akidar cin zarafin mata da ‘yammata dake daukar sabon salo a kowane lokaci a sassan Najeriya.
Ta ce la’akari da kima da daraja wadannan shugabannin a cikin al’umma babu shakka zasu iya kawo sauyin da zai bada nasarar da ake bukata.
Shugabannin gargajiya dana al’uma da kuma shugabannin addinai daga jihohin Najeriya da suka hallara a zauren taron, sun yi mahawara da musayar ilimi kan gudunmawar da kowa ya kamata ya bayar domin kawo karshen kalubalen da mata da ‘yammata ke fuskanta a Najeriya.
Malam Bashir Adamu Aliyu ne ya wakilci zauren malaman Kano har-ma ya gabatar da makala wadda ta maida hankali akan yin aiki da dokokin da addinai suka shimfida na bada kariya ga mata da kuma mutunta su.
A tsokacin sa, Reverend Istifanus Konce, guda cikin masu wa’azin kirista a Najeriya na cewa, cin zarafin mata da ‘yammata babban zunubi a addinin kirista kuma duk wanda bai kiyaye da haka ba, babu shakka zai fuskanci matsala a lahira.
A makalar data gabatar, Farfesa Aisha Abdul Isma’il tsohuwar Daraktar Cibiyar nazarin jinsina ta Jami’ar Bayero Kano, ta nanata cewa dole a maida hankali wajen rubuce rubucen dake fayyace banbancin ala’adun mutane da addinan su, musamman la’akari da yadda wasu mutane ke yiwa addini da al’ada kudin goro a duk lokacin da wasu a cikin al’umma suka aikata badala.
Bakin mahalarta taron dai ya zo daya wajen bukatar hada hannu wuri guda domin kakkabe mummunar akidar cin zarafin mata da ‘yammata ta kowace fuska.
Ga dai sautin rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano: