Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC da wasu zasu gurfanar da gwamnan Gombe gaban kotu


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Gombe da kungiyar dake kare salon mulkin dimokradiya zasu gurfanar da gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo gaban kotu bisa sake sabunta wa'adin shugabannin riko na kananan hukumomi maimakon ya gudanar da zabe

Jam'iyyar da kungiyar zasu kalubali hukuncin da gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo ya yanke na kara wa'adin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar har tsawon watanni shida karo na biyu a jere.

Abdullahi Muhammad Inuwa masanin shari'a kuma mai kare salon mulkin dimokradiya ya bayyana matsayinsa akan batun. Abun da gwamnan ya yi abu ne da ya sabawa kundun tsarin mulkin kasa kuma yiwa kara tsaye ne ga mulkin dimokradiya a Najeriya. Matsayin gwmnan ya sabawa rantsuwar da ya yi na kama aikin ofishinsa. Ya rantse ba zai nuna fifiko ga kowane bangare amma amma gashi ya yi, ya kuma bar wani bangare ba madafi. Yace ya ba gwamnan sati daya ya janye abun da ya yi ko kuma su hadu a kotu wurin neman fasara.

A cewar Barrister Inuwa kundun tsarin mulkin kasar bai ba majalisar dokoki ikon sabunta wa'adin shugabannin kananan hukumomi ba. Ko su 'yan majalisar ba zasu iya kara wa'adinsu ba matuka ya kare.

Alhaji Sale Tinka jigo a jam'iyyar APC reshen jihar yace abun da gwamnan ya yi cin mutuncin 'yan jihar ne. Ba zasu yadda ba domin ba jam'iyya daya ke Najeriya ba wadanda kuma ya nada duku 'yan jam'iyya daya ce. Yin hakan bai ba mutane 'yancinsu ba.Dole a yi zabe duk wanda mutane suka zaba shi ke nan. Zasu garzaya kotu domin neman 'yancinsu.

Amma ta bakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasiru Nono dokar zabe ta jihar ta bada dama gwamnan ya yi hakan. Dokar ta bashi damar ya nemi izinin majalisar ya sake nada shugabannin riko na kananan hukumomi har zuwa lokacin da za'a samu a yi zabe.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG