Wata baraka ta kunno kai tsakanin shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Borno akan tsayar da Modu Sheriff shugaban jam'iyyar na kasa.
Tun a makon jiya ne aka bayyana Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa lamarin da ya sa kwararrun harkokin siyasa suke ta tofa albarkacin bakinsu game da nadin.
Zaben Sanata Modu Sheriff ya gamu da suka da dama daga cikin gida da waje. Amma akwai wasu da suka yi na'am da nadin. A makon jiya shugaban PDP na reshen jihar Borno Alhaji Babab Basharu ya fito baro baro ya yi watsi da nadin yana cewa su basu san da zaben ba.Yace basu amince da nadin ba.
To saidai a wani bangaren na jam'iyyar a cikin jihar Borno a karkashin jago rancin sakataren jihar Alhaji Usman Madi Baderi sun kira taron manema labarai suka ce shugaban jam'iyyar na jihar ya fadi ra'ayin kansa ne. Sun hakikance ba da yawunsu ya yi magana ba. Ra'ayinsa ya fada inji sakataren.
Shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomisun ce su suna goyon bayan zaben Modu Sheriff. Alhaji Sheriff Mustapha shi ne shugaban gamayyar shugabannin PDP na kananan hukumomi yace sun goyi bayan zaben Modu Sheriff.
Ga karin bayani.