Kama daga kwamitin amintattu da kungiyar tsoffin ministocin PDP da wasu tsoffin jami’an kamfen din tsohon shugaba Jonathan, musammam ma Femi Kayode. Yawancin masu adawar sun dawo suna cewa kodai basa mara baya ga Sharif din ba wani mataki da zasu iya dauka fiye da nuna damuwa, tunda basu da hurumin kada kuri’a ga kwamitin da ya zabi Sharif din.
Shugaban kwamitin amintattun PDP Walid Jibrin, yace a lokacin da akayi zabe Modu Sharif ya samu 60 sauran mutane 4 da sukayi takara da shi sun sami 11 kawai.
Jaridun Najeriya sun rawaito tsohon ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki, na cewa ya tabbatar tsohon shugaba Jonathan baya marawa Sharif din baya, amma Sharif yace shi a sanin sa Jonathan ya kira shi yayi masa murna kuma sun zauna sunyi maganar yadda za a ciyar da jam’iyyar gaba.
Domin karin bayani.