Cikin wannan makon ne dai Jami’an Majalisar Koli ta Jam’iyyar PDP suka share wuni guda har suka zabi shugaban jam’iyyar daga Arewa maso Gabas ta Najeriya, inda daga karshe tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sherif, ya zamanto shugaban Jam’iyyar.
A wata hira da wakilin Muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari yayi da Modu Sherif, sabon shugabagaban jam’iyyar adawan yace abin da zai sa a gaba yanzu a matsayinsa na shugaban jam’iyyar shine zai bi duk ‘ya ‘yan jam’iyyar da suka fice wadanda suka taimaka aka kafa jam’iyyar da su, su dawo gida domin a sake gina ta.
Shugaban yace fushi ne yayi sanadiyar ficewar wasu ya yan jam’iyyar wanda dole ne a bisu a basu hakuri, har ma ya kara da cewa aikinsa a matsayinsa na shugaba shine ya baiwa kowa hakuri domin a sake gina jam’iyyar ta dawo kamar yadda take a baya.
Saurari hirar.