A jamhuriyar Nijar kwararru a fannin dokokin tsarin mulki daga kasashen Afrika da na Turai sun soma wani taron nazari akan tsarin ayyukan kotunan tsarin mulki da zummar bullo da wani kundin da zai taimaka a shayo kan matsalolin da ke dabaibaye shara’ar rigingimu ‘yan siyasa.
Kasar Nijar na cikin kasashen da bangarorinsiyasa ke yawan shigar da karan juna a gaban kotun tsarin mulki domin a warware wani kullin da ya kawo cijewar al’amura walau a tsakanin adawa da masu rinjaye a majalisar dokoki ko kuma a tsakanin majalisar dokoki da bangaren zartarwa. Dalili kenan da kungiyar ANDC ta masanan dokokin tsarin mulki ta ga dacewar shirya wannan taro.
Sau tari a kan zargin alkalan kotunan tsarin mulki a kasashen Afrika da nuna bangaranci musamman taka rawa da bazar masu mulki wajen yanke hukunci .
To ko wace gudunmawa wannan taro zai bayar domin kawo karshen irin wannan tunani ? Dr MAINA BUKAR KARTE Kwarar ren masani ne na dokokin tsarin mulki.
An dai gayyato ‘yan farar hula da ‘yan siyasa a wannan haduwa cikinsu har da ABUBAKAR SABO wakilinjam’iyu masu mulkin Nijar.
Taron na tsawon kwanaki 3 na matsayin wani fagen mahawarar kwararru daga jamio’in kasashen Senegal Cote D’ivoire, Benin, Burkina Faso, Afrika ta Kudu,Nijar da Faransa.
Ga karin bayani.