An cimma wata matsayar tsagaita wuta a fadan da ake yi a Tripoli babban birnin Libya, yayin da ake fara bukuwan sallar layya.
Shugaban dakarun Libyan Natioanl Army Khalifa Haftar, ta amince da wannan yarejejeniya, wacce Majalisar Dinkin Duniya ta bukata a kulla a yau Asabar, kamar yadda mai mai magan da yawunsa, Ahmad Al Mesmari ya fada a wani taron manema labarai a Benghazi.
Tun da farko dama, gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, ta yi na’ama da wannan matsaya da aka cimma domin a samu a yi bubkuwan salla da za a fara a gobe Lahadi.
Tun dai daga watan Afrilu ake ta gwabza fadan neman karbe ikon birnin Tripoli tsakanin dakarun Haftar da na gwamnati, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum dubu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta tabbatar.