Da alamu matsalar tsaron da ake fuskanta a kasar Mali, ita ce ta hana mutane shigowa da dabbobinsu domin cin kasuwar sallah a jamhuriyar Nijar.
Ya yin da ya rage saura mako guda ayi babbar sallah, wakilin Muryar Amurka, Sule Muminu Barma, ya ziyarci kasuwar dabbobi ta Turaku, ya fuskanci rashin hada-hadar kasuwanci irin wadda aka saba yi a baya.
Halin ‘karancin abincin dabobi da aka yi fama da shi a bana, ya haifar da matsalar karancin dabobi a kasuwanni inji Abdullahi Yahahai, mai sana’ar sayar da dabbobi.
Shiga da fice tsakanin Mali da Nijar sun ragu matuka, sanadiyar tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a arewacin Mali, lamarin da ya haddasa tsoro a zukatan mutane musammanma ‘yan kasuwa dake harkokinsu a kasashen biyu.
Matsin tattalin arzikin da kasar Nijar ke fama da shi a halin yanzu, ya jefa magidanta da dama cikin ‘kangin fatara lamarin da ya sa wasu daga cikinsu ke ganin samun abin yanka a bana sai yadda hali ya yi.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum