Sallar Eid-el-Kabir a bana ta kasance ranar Jumma’a da ba kasafai ake samun yin sallar Idi rana guda da sallar Jumma’a ba.
Al’umma da dama sun nemi sanin ko zasu gudanar da sallar Idi da sallar Jumma’a?
Sheik Abubakar Bala Imam Gana, daraktan ilimi na kungiyar JIBWIS a jahar Filato yayi kokarin bayyana fatawar da ta warware matsayin sallar idi da ta Juma’a idan sun hadu rana guda.
Ya ce fatawar Maliki da Abu Hanifa ra’ayinsu daya ne wanda ya ce idan da hali a yi sallar Juma’a da kuma idi, amma Shafi’i ya ce idan aka yi sallar idi ba a yi sallar juma’a ba rufsa ne.
A babbar sallah ne dai ake yin layya. Salisu Shehu, wani mai saida raguna ya ce farashin dabbobin bai ya tsanani ba, shi kuma Muhammad Sani ya ce an tsauwala kudin ragunan a bana.
Malam Muhammad Auwal Ishaq ya ce ba dole sai al’umma sun yi layya da rago ba, ana iya yi da akuya, ya kara da cewa kowa na iya yi gwalgwadon halin da Allah ya hore masa.
Gwamnatin jihar Filato ta umurci al’ummar musulmai su gudanar da sallar idi a masallatan Juma’a don rage yaduwar cutar coronavirus.
Saurari rahoton Zainab Babaji.
Facebook Forum