Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Daf Da Kafa Sabuwar Gwamnati  A Syria Bayan Arcewar Assad


Hambararren shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Hambararren shugaban kasar Syria Bashar al-Assad

Rayuwa ta ci gaba a Damascus a yau Litinin a daidai lokacin da aka bude sabon babi cike da fata da rashin tabbas bayan da ‘yan tawaye suka kwace babban birnin kasar Syria sannan shugaba Basar Assad ya arce zuwa Rasha bayan shafe shekaru 13 ana gwabza yakin basasa da fiye da shekaru 50 na bakin mulki

Cunkoson ababen hawa ya dawo kan tituna kuma mutane sun fito harkokinsu bayan dokar takaita yawon dare, saidai galibin shaguna sun kasance a rufe. ‘yan tawaye na sintiri a tsakiyar birnin.

SYRIA
SYRIA

Firdous Omar, daga yankin Idlib na arewa maso yammacin Syria na cikin mayakan da suka mamaye dandalin Umayyad, yace tun a shekarr 2011 yake yakar gwamnatin Assad yanzu kuma yake fatan ajiye makaminsa tare da komawa kan sana’arsa ta aikin gona.

A da muna da buri da manufar da muka sanya a gaba yanzu kuma mun cimmasu. muna so gwamnati da jami’an tsaro su karbi ragamar gudanar da al’amura.”

Hanzarin da gamayyar kungiyoyin mayaka karkashin jagorancin kungiyar HTS, tsohuwar kawa ga al’ka’ida, suka karbe iko a Syria, ya zamo wani muhimmin abin tarihi a Gabas Ta Tsakiya.

Hakan ya kawo karshen kisan dubun dubatar mutane, daya haddasa matsalar ‘yan gudun hijira mafi girma a wannan zamani tare da mayar da birane bangori saboda hare-haren bama-bamai, da kuma mayar da tarin kauyuka kufayi sannan takunkuman da duniya ta kakkabawa kasar suka durkusar da tattalin arzikinta.

Wasu mutane suna layin sayan burodi a Syria, bayan an hambare Bashar al-Assad a Damascus, Dec. 9, 2024.
Wasu mutane suna layin sayan burodi a Syria, bayan an hambare Bashar al-Assad a Damascus, Dec. 9, 2024.

A karshe dai milyoyin ‘yan gudun hijira na iya komawa gida daga sansanoninsu dake warwatse a kasashen Turkiya da Lebanon da kuma Jordan.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG