Firaministan Burtaniya Theresa May, na fadi-tashin ganin ta ja hankalin mukarraban gwamnatinta, domin su goyi bayan daftarin yarjejeniyar ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar turai, wanda masu shiga tsakanin kasar suka kwashe watanni suna kai-ruwa-rana, da takwarorin aikinsu na bangaren tarayyar Turai.
Sai dai wannan daftari mai shafi 500, na ci gaba da haifar da sabani a tsakanin ‘yan jam’iyar Conservative, mai mulki da kuma jagoranci a Majalisar Dokokin Burtaniya, wacce ita za ta yanke hukunci a karshe kan wannan lamari.
Yayin da rahotanni suka fara nuna cewa an cimma wata matsaya, ‘yan gani-kasheni masu goyon bayan ficewar kasar daga tarayyar ta turai, sun soki yarjejeniyar wacce aka kulla da tsohon ministan harkokin wajen Burtaniya Boris Johnson, da ya yi murabus daga mukaminsa a farkon shekarar nan.
Su ma dai manyan jam’iyyun adawan kasar ta Burtaniya sun soki wannan yarjejeniya, wacce ya zuwa yanzu ba a wallafa ta ba.
Facebook Forum